Muhimman Abubuwa Bakwai na Rayuwa

Ya faru shekaru da dama da suka wuce lokacin ina ɗan shekaru ashirin. na kasance cikin mota mai ƙetara ƙasashe, ina tafiya daga gidana da ke Dallas, Texas, don shiga kundin ƙwarewa na gargajiya a Charlevoix, Michigan. Ina da lokaci mai yawa don tunani lokacin da na hau motar tafiyata, ta cikin motar da ke ƙetara jihohi, na nuna damuwa, ina duban gonakin alkama da muka wuce a kan hanya.

Can, sai na fara tunani game da dukan ayyuka da na ke ciki, da kuma ɓangarori daban-daban na rayuwata. Shin dukkanin abubuwa ne kawai? ko kuma duk abin nufi ne don haɗuwa ko ta halin ƙaƙa? Shin wasu ayyukan sun fi na sauran abubuwa? Shin ina bada lokaci ga abubuwa masu muhimmanci a cikin dogon lokaci, ko kuwa ina raunana rayuwa ba da lokaci da makamashi da yawa ga abubuwan da ba za su taɓa amfani da ni ba, kuma ba za su taba zama wani abu na ainihi ba?

Na san cewa lallai ina son rayuwata ta karfafa. Na so in kashe mafi yawan rayuwata a kan abin kirki, ban so in zo ƙarshen rayuwata ba in kalli baya, kuma in yi matuƙar damuwa game da zubar da ƙullun rayuwata. Ba na so in zo ƙarshen lokacina a duniya kuma in gane da zurfin baƙin – ciki cewa na busa shi; cewa na rasa damar da zan samu a rayuwata ta yadda zan iya zama cikakke, har ma mahimmanci --- duk burina da mafarkai, da yin tasirin da ba kawai zai zama mai lada ga kaina ba, amma zai wadata rayuka da kuma abubuwan da suka shafi mutane da yawa.

Don haka na ɗauki lokaci don lissafin duk ayyukan da na ke buƙata don sanin ko na yi amfani da mafi kyaun lokacina don gano ayyukan da ake buƙatar ƙarin lokaci, da mayar da hankali da kuma kulawa. Sannan kuma wasu ayyukan za su buƙaci in bari, ko kuma in cire su daga rayuwata.

Kamar yadda jerin ayyukana suke girma kullum, ya zama bayyananne cewa kusan dukkanin ayyuka na sun faɗi cikin wasu ƙananan jinsi. Na ƙuntata ƙananan ɗakunan zuwa bakwai. Bayan haka, yayin da na mayar da hankali kan ƙoƙarin gano abubuwan da suka fi muhimmanci, na kwatanta jinsin don sanin ƙayyadadden muhimmancin rayuwata.

Na kasance da damar gabatar da waɗannan sassa guda bakwai bisa ga muhimmancin zamunta, tun daga wannan lokaci shekaru da dama da suka wuce, waɗannan muhimmancin ba su taɓa raunana a cikin muhimmancin zumunci a rayuwata ba.

Wannan shi ne tsarin tunanina.

Allah shi ne farko. Shi ya haliccemu. Ya nubuta dokoki na rayuwa. Fahimtar Allah shi ne fahimtar rayuwa. Ganin rai daga hangen Allah yana kawo fahimta. Sanin shi, da fahimtar sanin shi, da fahimtar shi babban abu ne. Wannan nassi ya ƙarfafa inda aka rubuta cewa, “Kadda ku kasance kuna da wasu alloli a gabana” (Fitowa 20:3) kuma “Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyar da dukai ranku da dukan hankalinku da ƙarfinku. Wannan shi ne doka na farko” (Markus 12:30).

Abu na biyu yana da muhimmancin gaske ga hali na da ɗabi’una, rayuwata na daga cikin samfurin zaɓina a ƙarshen lokacin da aka kira ni in ba da lissaafin rayuwata da kuma yadda na rayu da shi, cikakken alhakin zai kasance tare da ni. Kuma tun lokacin da na zaɓa daga cikin halin kaina da mutuntaka, dole ne in mayar da hankalin gaske game da kasancewa mafi kyaun mutumin da zan iya zama – mutumin da zan fi sha’awarsa. Yana da mahimmanci a gare ni in ɗauki alhakin kaina kuma in kasance mai tasiri wajen bunƙasa halin kaina saboda wannan zai shafi duk wani wuri na rayuwa ta kamar yadda Yesu ya ce, “ka fara cire ɗan kwarin daga idonka, sa’an nan za ka gani a fili don cire tsinke daga cikin idon ɗan-uwanka” (Matiyu 7:5).

Bayan yanayin hali, har yanzu akwai wasu wurare masu muhimmanci na rayuwa amma mafi muhimmanci ya ƙunshi wasu mutane. Kamar yadda Yesu ya ce, “na biyu kuma shi ne ƙaunar maƙwabcinka kamar kanka” (Matiyu 22:39). A lokacin yin la’akari da damgantaka da mutane, ‘yan-uwa dole su zo gaban wasu a cikin fifiko saboda an sanya ni kai tsaye a kan su ta wurin haihuwa ko aure. Yin haɗi tare da wani ta wurin (jini) haihuwa ko aure ya ba da umarni da karfi da kuma alhakin kwarewa. Alal misali lokacin da Yesu yana mutuwa a kan gicciye, ya ɗauki lokaci don ya umurci Yohana ya tabbatar cewa an kula da mahaifiyarsa (Yohaana 19:26-27). “Amma idan wanda ba ya kula da danginsa, kuma yana ƙaunar iyalinsa, ya ƙi bangaskiya kuma ya fi muni marar gaskiya” (1 Timothawus 5:8).

Bayan iyali, sai dangamtaka da hulɗa tare da wasu mutane wannan ya haɗa da abokai, da magabata na hukumomi kamar ma’aikata, shugabannin ruhaniya (addini) da jami’an gwamnati, da kuma haɗin kai da abokan arziki da sauransu.

Baya ga mutane, sai abubuwa uku na alhakin kiwon lafiya, aiki da sha’anin kuɗi, a cikin wannan tsari kiwon lafiya yana gaba ga aiki, saboda dole ne ka lura da lafiyar jikinka don ka samu yin aikin kirki. Idan ka rasa lafiyar jikinka, ba za ka iya cika haƙin alhakin aiki ba.

A ƙarshe, akwai alhakin kuɗi da mallaka. Waɗannan suna da mahimmanci, amma ba su ne za a fi mai da hanƙali garesu ba a rayuwa. Ba sa ba rayuwa ma’ana ba, ko kuma su ba shi dalili kamar yadda aiki ke yi ba. Suna ba da mataki taimako ne su na ba da tabbacin hanyar samu don cika hakkin rayuwa mafi muhimmanci.

Ga shi nan/ka gani kamar yadda na gani, duk alhaki da ayyukan rayuwa sun shiga jinsi bakwai. Idan aka tantance ayyukan da alhakin a jerin ma fi fifiko ga yadda za su faru.

1. Allah, tare da dukkanin abubuwa na ruhaniya da rai na har abada. Wannan ya shafi fahimtar abubuwa da suka shafi Allah, da rai na har abada da Allantaka da abubuwan ruhaniya.

2. Hali, wanda ya shafi ginin hali da ganowar ainihin – kai, wato ni wane ne, kyautata, da/baiwata,da karfina da alhakin halayyata, da dalilin zaɓina da tunani na

3. Iyali, wanda ya ƙunshi alhakin aure, da iyaye da sauran zamantakewa na iyali.

4. Abokai da Abokan Arziki da Hukumomi. Wannan rukuni na da faɗin gaske don ya shafi dukkanin hulɗoɗin mutum da dangantaka waɗanda suke wajen iyali. Ya shafi dukan abubuwanka na haɗuwa da jama’ar da ka sani da kuma baƙi da abokai da hukuma. Na san cewa idan muka duba dukan huldarmu da idon samun abin kirki za mu gane duk haɗuwar mu da abokan arziki,da abokai,da hukuma har ma da baƙi. za mu ga cewa yana da amfani.

5. Kiwon Lafiya, wanda ya haɗa da dukkan nau’in lafiyar jiki, da ciki har da abinci, da motsa jiki da damuwa da matsaloli. Ya kamata a kiyaye lafiyar jiki don mu sami cikakken sanin duk abin da rai ke riƙe mana da shi.

6. Ayyuka, Manufa da Kaddara. Wannan ya haɗa da dukkan aikin da ke ba da ma’ana a rayuwarmu da kuma dalilai don farkawa (tashi daga barci) ko wace safiya. Wannan ya haɗa da aiki, da buƙatu abubuwan da suke haifarwa da kuma ayyukan fasaha.

7. Ma’aikatar kuɗi da Kasuwanci. Wannan rukunin al’amuran da suka shafi kuɗi da gidaje da motoci da sauran kayan dukiya ne, ba don burin da za a yi da su ba,sai don albarkatun da za a yi amfani da su don tallafawa mana yayin da muke ƙoƙarin cika wasu manufofin da suka fi muhimmanci.

Idan ka dauki lokaci don tunami game da wannan, za ka ga cewa duk abin da ke cikin rayuwarka yana ɗaya daga cikin waɗannan yankunan da na yi. Na yi tunani, na sake yi, na dauki lokaci na yi tunani sosai game da wannan al’amari.

Waɗannan hanyoyi guda bakwai na rayuwa kamar yadda na ga abubuwa, su ne manyan nau’i bakwai na sirrin alhaki.

Amma kai, mene ta ra’ayinka? Ka yarda? Abu mafi muhimmanci shin ka ɗauki lokaci ka dakata ka yi tunani game da ayyukan rayuwa da kuma muhimmancin ayyuka daban-daban na rayuwarka? Wannan zai iya zama mafi amfani abin da zai fito daga karanta wannan ɗan rubutu. Na roƙe ka, ka yi tunani game da rayuwarka. Shin kana bin hanya madaidaiciya cikin wannan tafiyarka ta makoma? Ko kuwa kana buƙatar gyara? Duk lokacin dake wucewa na da amfani fiye da tunaninmu! Yi zaɓin kirki abokina.